Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A Nigeria har yanzu ba a kai ga matsayin da ake bukata kuma masu koyarwa da masu koyan karatun kur'ani mai girma ba a bas u kulawar da suke bukata domin har yanzu ana amfani da salo da tsarin karatun kur'ani mai girma irin na galgajiya na iyaye da kakannu.A wata tattaunawa da ta hada Ibrahim Musa wani mai taka rawar gani a harkokin da suka shafi addinin musulunci a Nigeria ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya kara da cewa; a bias al'ada kur'ani ana fara koyar das hi ga yaro dan shekaru hudu a duniya da zarar ya fara iya Magana kuma yana iya fahimtar ayoyin kuma yana fara wa ne da ayoyi kanana ko surori kanana . Kuwa yawancin yankuna na arewacin Nigeria haka lamarin yake suna fara koyar da yayansu da kais u makaranta tun suna kanana kuam wannan tsari yana ci gaba da wakana babu wani sauyi ma'ana ana ci gaba da bin wannan tsari irin na galgajiya babu wani sauyi ko canji kan haka neman da dama daga cikin masu bin diddigin wannan tsari suke ganin lokaci yayi day a kamata a kawo sauyi da canji a cikin wannan tsari na koyar da karatun kur'ani mai girma a Nigeria.
1002009