Bangaren kasa da kasa; sakamakon wani bincike da aka gudanar a wata cibiya ta kwararru kan binciken masu sauraron gidajen radiyoyi a kasar Marokko ya fitar da samakon bincikensa da a ciki ya bayyana cewa daga cikin gidajen radiyoyi da ake saurara a wannan kasa ,radiyon kur'ani ne yafi yawan masu saurare da hakan ke nufin cewa yawancin al'ummar kasar na yin riko da addinin musulunci ne kuma ana kara samin masu ra'ayin addini da riko da addinin musulunci da kuma kur'ani a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; sakamakon wani bincike da aka gudanar a wata cibiya ta kwararru kan binciken masu sauraron gidajen radiyoyi a kasar Marokko ya fitar da samakon bincikensa da a ciki ya bayyana cewa daga cikin gidajen radiyoyi da ake saurara a wannan kasa ,radiyon kur'ani ne yafi yawan masu saurare da hakan ke nufin cewa yawancin al'ummar kasar na yin riko da addinin musulunci ne kuma ana kara samin masu ra'ayin addini da riko da addinin musulunci da kuma kur'ani a wannan kasa.Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta yabilad an watsa rahoton cewa: mashahuriyar cibiyar bincike kan masu sauraren gidajen radiyoyi da talbijin a kasar marokko a ranar sha tara ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani taron manema labarai dangane da bayyana sakamakon binciken da ta gudanar ta bayyana cewa; kimanin kasha sha tara cikin dari na masu sauraren radiyoyi a kowace rana kimanin awa biyu da rabi ne suka yin a sauraren radiyon kur'ani da hakan ya sa radiyon kur'ani ya kasance a sahun gaba na wadanda suke sauraren gidajen radiyoyi a wannan kasa kuma wannan babban lamari ne mai muhimmancin gaske musamman a daidai wannan lokaci da ake ciki .
1004129