IQNA

Hare-Haren Ta'addancin Damascus Na Ci Gaba Da Fuskantar Allawadai Daga Al'ummomin Duniya

21:14 - May 12, 2012
Lambar Labari: 2324060
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban majalisar mabiya tafarkin shi'a a kasar Lebanon ya yi kakausar suka da yin Allawadai da kaoii harin ta'addanci a kan fararen hula da jami'an tsaro a birnin Damascus na kasar Syria da nufin kawo fitina tsakanin al'ummomin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, Ayatollah Abdulamir Qabalan mataimakin shugaban majalisar mabiya tafarkin shi'a a kasar Lebanon ya yi kakausar suka da yin Allawadai da kaoii harin ta'addanci a kan fararen hula da jami'an tsaro a birnin Damascus na kasar Syria da nufin kawo fitina tsakanin al'ummomin kasar saboda matsayin gwamnati na goyon bayan gwagwarmayar musulunci.
A nata bangaren kuwa Rasha ta bukaci kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ya dauki kwararan matakai na hana yin fasakwabrin makamai zuwa cikin kasar Syria matukar dai da gaske ne ana bukatar kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Elexender Lokachvich ne ya bayyana hakan, inda ya ce Rasha ta yi imanin cewa makaman da wasu kasashe ke aikewa da su zuwa ga 'yan tawaye da ma kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria hakan ba maslaha ce gare su ba, kamar yadda hakan ba maslaha ce ga al'ummar Syria ba wadanda ake kashewa kullum rana da wadannan makamai.
Ya ce rasha tana da masaniya kan kame wani jirgin ruwa shakare da muggan makamai da sojojin Lebanon suka, wanda ya fito daga kasar Libya zuwa ga 'yan tawayen Syria, daga cikin abubuwan da yake dauke da su ba ya ga manyan bindigogi da makaman roka da RPG, har da sanadarai na hada bama-bamai, ya ce kasashen da suke yin hakan su kwana da sanin cewa, abin da suke yi ya yi hannun riga da shirin zaman lafiya a Syria, wanda Kofi Annan ke jagoranta.
1005055
captcha