IQNA

An Bude Ajujuwan Koyar Da Tafsirin Kur’ani Mai Tsarki A Husainiyyar Baqiyatollah

14:42 - May 19, 2012
Lambar Labari: 2329127
Bangaren kur’ani mai tsarki, an bude ajujuwan koyar da tafsirin kur’ani mai tsarki a husainiyyar baqiyatollah da ke birnin zaria a arewacin tarayyar Nigeria da nufin fara shirin fuskantar lokacin azumi mai zuwa wanda dukkanin musulmi suke sauraron karatu da tafsirin kur’ani mai tsarki a fadin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na bangaren yada labaransa a nahiyar Afirka cewa an bude ajujuwan koyar da tafsirin kur’ani mai tsarki a husainiyyar baqiyatollah da ke birnin zaria a arewacin tarayyar Nigeria da nufin fara shirin fuskantar lokacin azumi mai zuwa wanda dukkanin musulmi suke sauraron karatu da tafsirin kur’ani mai tsarki a fadin kasar wadda ke da yawan musulmi.
A yayin karatun shugaban harkar musulmunci malam Ibrahim Zakzaky ne ya jagoranci bude wadannan ajujuwa wanda malamai suke bayar da gudunmawarsu wajen koyar da mutane wannan salo na karatu da tafsirin kur’ani mai tsarki, karatun dai ya kasance a cikin matakai, inda wasu kan samu horo na bangaren kur’ani daga kanan surori, wasu kuma gwargwadon yadda za su iya fahimta da kuma koyar da sauran mutane.
Bude ajujuwan koyar da tafsirin kur’ani mai tsarki a husainiyyar baqiyatollah da ke birnin zaria a arewacin tarayyar Nigeria da nufin fara shirin fuskantar lokacin azumi mai zuwa wanda dukkanin musulmi suke sauraron karatu da tafsirin kur’ani mai tsarki a fadin kasar, hakan na matukar muhimmanci, domin kuwa zai bayar da damar yin shirin da ya kamata kafin zuwan lokacin. 1010728
captcha