IQNA

Jinjinawa Kan Fatawar Jagora Da Kuma Farfagandar Yammaci kan Tattaunawa

17:43 - May 22, 2012
Lambar Labari: 2331878
Bangaren siyasa: wani mamba a komitin ilimi kuma mai sharhi kan harkokin siyasa da abubuwan da ke wakana a duniya kan fatawar da jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ya fitar na haramta mallakar makamin nukliya ya bayyana cewa: a daidai lokacin da wannan fatawa ke bawa kasashen yammaci tabbaci da nucuwa kan Iran bat a da niyar mallakar makaman nukliya sai gashi a dayan bangare suna yada farfagandan karya cewa matsin lambarsu ne ya tilasta Jamhuriyar musulunci ta Iran daukan wannan mataki.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci taIran ne ya watsa rahoton cewa: wani mamba a komitin ilimi kuma mai sharhi kan harkokin siyasa da abubuwan da ke wakana a duniya kan fatawar da jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ya fitar na haramta mallakar makamin nukliya ya bayyana cewa: a daidai lokacin da wannan fatawa ke bawa kasashen yammaci tabbaci da nucuwa kan Iran bat a da niyar mallakar makaman nukliya sai gashi a dayan bangare suna yada farfagandan karya cewa matsin lambarsu ne ya tilasta Jamhuriyar musulunci ta Iran daukan wannan mataki.Muhammad Sadik Kushki a wata tattaunawa ce da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na ikna ya bayyana cewa: a maimakon kasashen yammaci da kuma gwamnatocinsu su yi afani da wannan damar wajan warware wannan takaddama da tabbaci da Iran tab a su sai gashi sun ci gaba da yin riko da hanyar da suka saba ta makirci da danne hakkin sauran kasashen duniya da hakan ba wani alheri ne hatta a gare su face bata lokaci da yin riko da siyasar yaudara da bata lokaci .Kuma kasashen biyar masu kujerar dindindin ta hawa kujerar naki a komitin tsaro na majalisar dinkin duniya gami da Karin kasar Jamus sun san da haka da gaskiyar jamhuriyar musulunci kan shirinta na nukliya na zaman lafiya ne ban a mallakar makamin nukliya ne ba.
1012926
captcha