IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Mai Tsarki Ta Matasa A Birnin Moscow

20:48 - June 08, 2012
Lambar Labari: 2342132
Bangaren kur’ani, an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Engels na yankin Saratov a kasar Rasha inda daliban makarantun musulmi musamman na kur’ani suka gudanar da gasa atsakaninsu kuma an bayar da kyautuka ga dukkanin daliban da suka nuna kwazo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a cikin makon nan ne aka gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Engels na yankin Saratov a kasar Rasha inda daliban makarantun musulmi musamman na kur’ani suka gudanar da gasa atsakaninsu kuma an bayar da kyautuka ga dukkanin daliban da suka nuna kwazo a wajen wannan gasa.
a kasar Pakistan kungiyoyi da jam’iyyun siyasa na addini a kasar sun cimma matsaya kan kafa wani babban kawance guda daya wanda zai hada su baki daya ta yadda hakan zai ba su damar hada karfi da karfe domin tunkarar barazana da ke fuskantar mutane kasar daga makiya addinin musulunci a cikin wannan yanayi mai cike da rikici.
Yanzu haka an fara yin rijistar sunayen mutanen da suke bukatar gudanar da aikin hajjin bana birnin Lahour na kasar Pakistan wanda shirin yakegudana a halin yanzu babban husainiyar Minhaj da ke birnin kuma kofa bude take har yanzu mutanen da suke bukata tafiya ta wannan hanya a wannan shekara.
Kasar pakistan dai na daga cikin kasashen musulmi da suka fi yawan mabiya wanna addini, inda adadinsu ya kai sama da miliyan dari da saba’in, kuma suna samun gagarumin ci gaba da fuskar yada manufofi na addini ta hanyoyi da suka dace a zamannce kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar, wanda hakan ke tabbatar da ci gaban addini a yankin na kudancin nahiyar Asia.
1023987



captcha