Kamfanin dilalnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo cewa, yanzu ana shirin za a fara gudanar da gasa da karatun kur’ani mai tsarki wadda za ta kebanci daliban jami’a na kasar Iran a larduna na kasar kamar yadda za a girmama tare da bayar da kyautuka ga wadana suka nuna kwazo a dukkanin matakan gasar.
Shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar irin sauye-sauyen da ke faruwa a duniya wani lamari ne da ke nuni da cewa duniya ta kama hanyar tabbatuwar tsarin adalci.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Fonix ta kasar China inda ya ce tsarin da ke mulki a duniya a halin yanzu tsari ne da ke cike da zalunci da babakere kuma shi ne ummul aba'isin din irin koma bayan da al'ummomin duniya suke fuskanta da kuma hana su hakkokinsu. Don haka ne ma shugaban na Iran ya ce al'ummomi za su tabbatar da wadannan hakkoki na su ne kawai matukar suka ci gaba da yunkuri da kokari wajen dawo da su.
Yayin da aka tambaye shi kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, shugaban na Iran cewa ya yi matsayar kasar Iran kan wannan lamarin dai a fili yake, dukkanin ayyukan nukiliyan Iran yana karkashin sanya idon hukumkar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Shugaban ya ce matsala guda cikin wannan lamari shi ne yadda manyan kasashen duniya suka shigo da siyasa cikin lamarin.
1025074