IQNA

An Kai Hare-Haren Ta’addancin A Kusa Hubbaren Imam musa Kazim (AS) Da Ke Iraki

20:28 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346733
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan ta’adda sun kaddamar da harin ta’addanci kan masu ziyarar hubbaren imam Musa Kazim (AS) da ke kazimain a kasar Iraki da nufin sake dawo da yanayin da al’ummar kasar ta gania a baya na kisan kiyashin da ake yi wa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kaddamar da harin ta’addanci kan masu ziyarar hubbaren imam Musa Kazim (AS) da ke kazimain a kasar Iraki da nufin sake dawo da yanayin da al’ummar kasar ta gania a baya na kisan kiyashin da ake yi wa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Hare haren ta'addanci da aka kai a sassa daban daban na kasar Iraki sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 60 tare da jikkatan wasu fiye da dari na daban a yau laraba, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta bayyana cewa: Hare haren ta'addanci ta hanyar tada motoci biyu da aka makare da bama bamai a garin Hilla sun lashe rayukan mutane akalla 22 tare da jikkata wasu da dama.
Har ila yau tarwatsewar wasu motoci hudu da aka cika da bama bamai tare da kai hari ta hanyar harbi sun lashe rayukan mutane akalla 18 tare da raunata wasu masu yawa a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki, kuma an kai hare haren ne kan tawagar mutanen da suke kan hanyarsu ta ziyartar wajaje masu tsarki.
Haka nan an kai hari ta hanyar tarwatsa motoci biyu a garin Balad da suka yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla 4, kamar yadda hare haren suka jikkata wasu da dama.
1029192



captcha