Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al'alam cewa, an yi kira ga jami'ar Azhar da ta amince da mazhabar iyaan gida manzon Allah a hukumance domin kara tababtar da adin kai da fahimtar juna a tsakanin dukaknin bangarorin musulmi na duniya domin kuwa wannan jami'a ta dukaknin musumi ce na duniya baki daya.
A yau ne al’ummar kasar Masar suke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda ‘yan takara biyu da suka fi samun kuri’u a zabe zagaye na farko za su sake karawa, wato Muhammad Mursi na kungiyar Ikhwan da kuma Ahmad Shafiq tsohon pira ministan kasar a lokacin mulkin Husni Mubarak.
Kimanin mutane miliyan 50 ne dai suka cancanci kada kuri’a a kasar ta Masar, kuma zaben zai gudana ne a cikin kwanaki biyu, inda yanzu kimanin sojoji 150 gami da dubban ‘yan sanda suke cikin kyakyawan shiri, domin tabbatar da cewa zaben ya gudana lami lafiya a dukkanin fadin kasar, kuma ana sa ran sanar da sakamakon karshe na zaben a ranar 21 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.
A zaben da aka gudanar a zagaye na farko babu daya daga cikin ‘yan takarar da ya samu kashi 50% na dukaknin kuri’un da aka kada, duk kuwa da cewa dan takarar ikhwan Muhammad Mursi shi ne ya kasance a gaba da kashi 24.7% na dukaknin kuri’un, yayin da Ahmad Shafiq tsohon pira ministan Huzni Mubarak ke biye masa da kashi 23.6% na kuri’un, wanda hakan ya ba su damar zuwa zabe zagaye na biyu bisa ga ayar dokar zabe da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Masar.
Kasantuwar ‘yan takarar biyu da suka kai ga zagaye na biyu masu banbancin ra’ayi matuka, wannan ya sanya wasu daga cikin mutanen kasar zargin cewa mai yiwuwa akoma ga ‘yar gidan jiya matukar dai Ahmad Shafiq ya lashe zaben, kasantuwarsa babban jigo a cikin gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak da juyin juya hali ya kawar da ita a cikin watan Fabrairun 2011.
Yayin da wasu masu sassaucin ra’ayi suke ganin cewa masu kishin islama za su mamaye harkokin mulki da siyasa a kasar matukar dai dan takarar kungiyar Ikhwan Muhammad Mursi ya lashe zaben.
1030406