Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarea na yanar gizo na yada labaransa bangaren nahiyar Asia an fara wani shiri na horar da masu karatun kur’ani da za su iya shiga gasa ta karau da hardar kur’ani mai tsarki da za agudanar a kasar Kyrgystan a cikin watan Ramadan mai zuwa kamar dai yadda bangaren shirya gasar ya sheda a jiya agaban taron cibiyoyin mmuslunci na kasar wadda daya ce daga cikin muhimman kasashen musulmi da suke yankin.
Mabiya addinin muslunci a birnin New York na kasar Amurka sun gabatar da wata sharawa da nufin karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya da nufin samun fahimtar juna da zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu, da kuma kauce wa tuhumar juna da girmama rayoyin kowa.
A wani labarin kuma ana bayar da horon karatun kur’ani ga sojojin Burnei, daya daga cikin kasashen musulmi da suke bayar da matykar muhimamnci ga lamurra da suka danganci a ddinin muslunci a cikin dukaknin harkokin kasar, da suka hada da na gwamnati na jama’a daidauiku, da hakan ya hada lamurran soji na tsaro a kasar ta Burnei.
Gudanar da wani taron bayar da horo ga sojojin kasar Burnei kan karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda ta yadda hakan zai ba su damar sanin hanyoyon karfafa karatu da harda littafin mai tsarki yana da matukar amfani ga rundunar soji ta kasar musulmi, domin ko ba komai hakan zai ba su damar yin aikinsu bisa koyarwar addininsu.
1030454