IQNA

Salon Karatun Kur’ani Mai Sauki Shi Kansa Wata Fasaha Ce Mai Kima

22:02 - June 21, 2012
Lambar Labari: 2351505
Bangaren kur’ani, bin salo na karatun kur’ani mai sauki shi kansa wata fasaha ce mai zaman kanta wadda take da mtsayi da kima domin kuwa duk wanda yake da wannan fasaha zai iya amfanar da mutane da dama saboda ba kowa ne yake da wannan damar ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo cewa, bin salo na karatun kur’ani mai sauki shi kansa wata fasaha ce mai zaman kanta wadda take da mtsayi da kima domin kuwa duk wanda yake da wannan fasaha zai iya amfanar da mutane da dama saboda ba kowa ne yake da wannan damar ba ta yadda zai iya isar da wani sakonsa cikin hanya mai sauki.
A wani baynin kuma an gudanar da taron baje klin kur’ani a India, a wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara.
1034544

captcha