IQNA

An Bayyana Makarancin Kur'ani Mai Tsarki Na Iran A matsayin Wanda ya Nuna Kwazo

17:48 - June 28, 2012
Lambar Labari: 2356409
Bangaren kur'ani, an bayyana makarancin ur'ani na kasar Iran day a halarci gasa a bangaren harda zuwa mataki na karshe a matsayin wanda ya nuna kwazo ba wai kawai bangaren harda din ba kawai har ma da bangaren karatu da kyautata shi gami da tajwidi.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an bayyana makarancin ur'ani na kasar Iran day a halarci gasa a bangaren harda zuwa mataki na karshe a matsayin wanda ya nuna kwazo ba wai kawai bangaren harda din ba kawai har ma da bangaren karatu da kyautata shi gami da tajwidi kamar dai yadda daya daga cikin alkalan gasar ya bayyana.
Jagoran juyin juya halin musuluncin na kasar Iran Ayatullahi Sayyed Ali Khamene'i ya bukaci da a kara samun kyakkyawar mu'amala tsakanin bangaren gwamnati, na Majalisar Dokoki da kuma na shari'a domin samar wa kasar ci gaba a bangarori daban-daban na rayuwa.
Jagoran ya bukaci hakan ne a yau laraba, lokacin da yake ganawa da wasu manyan jami'a na ma'aikatar shari'a ta kasar a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasar Ayatullahi Sadiq Amoli Larajani, domin tunawa da zagayowar ranar da aka kai wani harin ta'addanci a shekarar 1981 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar manyan jami'an kasar ta Iran su 72 cikinsu kuwa har da alkalin alkalai na wancan lokacin Ayatullahi Mohammad Behesh-ti.

Har ila yau a lokacin wannan ganawa, jagoran na juyin musulunci ya tabo wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasar ta Iran da kuma na kasa da kasa, da suka hada da takun-sakar da ake yi tsakanin Iran da kuma wasu kasashe dangane da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya, inda ya jaddada cewa ci gaba da sarrafa makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya wani hakki ne na kasar Iran.

Ayatullahi Sayyed Ali Khamene'i ya ce duk da takunkumi da kuma sauran matakai na takurawa da wadannan kasashe ke dauka a kan Iran, a cewarsa hakan ba zai hana wa kasar samun ci gaba ba, wannan kuwa saboda irin goyon bayan da gwamnatin kasar ke samu daga al'ummar kasar.

1039215




captcha