IQNA

Amurka Da Gwamnatin Yahudawa Sune Kan gaba Wajen Fatali Da Dokokin Kasa Da Kasa

17:48 - June 28, 2012
Lambar Labari: 2356410
Bangaren siyasa, ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila su ne kan gaba wajen yin fatali da dokokin duniya musamman kan batun dokoki da suka shafi makamin nukiliya mallakarsu da kuma yadda za a kiyaye su.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila su ne kan gaba wajen yin fatali da dokokin duniya musamman kan batun dokoki da suka shafi makamin nukiliya mallakarsu da kuma yadda za a kiyaye su tare da yin kira da adauki mataki a kansu.

A bisa tsarin sabon takunkumin kauracewa man kasar Iran dai, kamfanonin da suke sayan danyen man fetur na kasar Iran, wadanda kuma suke biyan kudaden sayan man ta hanyar babban bankin kasar Iran, to gwamnatin kasar Amurka zata yanke mu'amala da su, ta kuma haramta masu hulda da dukkan kafafen mu'amala da bankunan kasashen Amurka.

Daga jibi Asabar din ne dai ake saran kasashen turai wadanda a shekarar bara suke sayan danyen mai fetur ganga dubu 450 a kowace rana daga kasar Iran zasu dakatar da sayansa. Hakama hukumar IAEA mai sanya ido a kan harkar makamshin nuclear a duniya ta bada sanarwa makonni biyu da suka gabata na cewa kasashen India, Japan, Koria ta Kudu da kuma China wadanda suka fi ko wace kasa sayan danyen man fetur daga kasar Iran sun rage yawan danyen ma da suke saya daga Iran da ganga dubu 350 a ko wace rana.

A bisa kididdigan hukumar makamashin kasar Amurka, a cikin watannin 6 na shekarar bara, kasar China ta saye danyen man fetur daga kasar Iran ganga dubu 555 a ko wace rana, Japan ganga dubu 341, India ganga 328, koriya ta kudu ganga 244 a ko wace rabna, wanda ya maidasu kasashen da suka fi sayan danyen man fetur daga kasar Iran a duniya.

Amma ganin yadda wannan takunkumin zai hargitsa tattalin arzikin kasashen duniya da dama, musamman kasashen da suka dugagara da danyen man fetur na kasar Iran don habaka tattalin arzikin kasashensu, ali tilasta kasar Amurka ta yi afwa ga wasu kasashen da abin ya shafa, inda ta lamunce masu kubuta daga takunkuminta ko da sun ci gaba da sayan danyen man fetur na kasar Iran bayan fara aiki da wannan takunkumin.

1039546


captcha