IQNA

14:07 - July 02, 2012
Lambar Labari: 2359211
Bangaren kasa da kasa;Yan tawaye yan salafiya da ke rike da arewacin kasar Mali sun lalata guraren addini da ziyara na garin Tumbuktu mai dadaden tarihi .


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Yan tawaye yan salafiya da ke rike da arewacin kasar Mali sun lalata guraren addini da ziyara na garin Tumbuktu mai dadaden tarihi .Wannan mataki ya fuskanci maida martini da yin Allah wadai daga kungiyoyi da dama tare da nuna rashin jin dadi matuka gaya kan yadda suka dauki wannnan mummunan mataki day a sabawa hankali da yancin dan adam da na addininsa kuma wannan wani lamari ne day a shafi gurbatacciyar akida ta salafiya da kokarin cusawa mutane ra'ayi da bakar akidarsu. A dayan bangare kuwa : Wata kungiyar masu daawar kishin Musulunci a arewacin kasar Mali mai suna Kungiyar Jihadi da tauhidi a Yammacin Afrika mai alaka da kungiyar Alkaida ta yi barazana wa kasashen da zasu ba da sojoji a rundunar sojin da zake shiryawa domin fatattakar yan tawayen kasar Mali.
Kakakin kungiyar Jihadin Adnan Abu Walid Sahrawi ya fadi a wani rubutaccen sako cewa rassan kungiyar a kasashe da dma suna shirye domin kai hari a kan kasashen da zasu bada sojoji wa rundunar ta ECOWAS.
A jiya Jumaa ne dai shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ta kasashe Yammacin Afirka suka yi zaman taron a kasar Ivory Coast domin yin nazarin yanda za a kawo karshen rikicin kasar Mali.
Kafa wannan runduna dai yana bukatar izinin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, kuma a zamansu na jiyan shugabannin kasashen ECOWAS din sun kirayi kwamitin da ya gaggauta amincewa.

1041905
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: