IQNA

An Gudanar Da Zama Kan Muhimman Batutuwa Da Suka Shafi Kur’ani

20:15 - July 02, 2012
Lambar Labari: 2359458
Bangaren kur’ani, an gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin malaman jami’an da kuma masana kan harkokin kur’ani a gefen wani taron baje kolin kayan kur’ani na duniya da aka gudanar da nufin kara bunkasa harkokin kur’ani tsakanin daliban jami’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa an gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin malaman jami’an da kuma masana kan harkokin kur’ani a gefen wani taron baje kolin kayan kur’ani na duniya da aka gudanar da nufin kara bunkasa harkokin kur’ani tsakanin daliban jami’a musamman a wannan lokaci da matasa suke kara buktuwa zuwa samun masaniya zuwa ga kur’ani mai tsarki.
A wani labarin kuma dakarun kare juyin juya muslunci a Iran sun fara gudanar da wani gagarumin atisayi a yau mai taken Rasul-a’azam 7 wanda za su gwada wasu sabbin makamai masu linzami da Iran ta kera gami da wasu na’urorin rada.
Babban hafsan dakarun kare juyi a bangaren mayakn sama Brigadier General Ali haji Zadeh ya fadi cewa, a cikin wannan atisayi da yardarm Allah dakarun kare juyin juya halin Musulunci za su makamai masu linzami da suka hada masu cin gajeren zango, matsakaicin zango da kuma dogon zango, daga cikinsu kuwa akwai wani sabon makami mai linzami da Iran ta kera wanda ke tafiyar kilo mita 150 a cikin kasa mintuna biyu, tare da samun abin da aka saita shi kansa ba tare da kure ba.
A bangare guda kuma Janar Ali Zadeh ya gargadi Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila kan yin gigin kaddamar da harin soji a kan Iran, domin kuwa yin hakan a cewarsa shi ne zai kawo karshen samuwar haramtacciyar kasar Isra’ila a bayan kasa.
1042132



captcha