Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo sarkin Jordan na ta fadi tashin ganin ya ceto masarautarsa daga boren fararen hula masunneman sauyi cikin harkokin mulki da siyasa a kasar da neman samun hukuma da mutane za su zaba da kansu maimakon zama karkashin tsari na mulukiya kawai wanda yay i hannun riga da abin da ake kira demokradiyya.
Kungiyar Hamas da hukumar cin gashin kan Palastinawa sun bukaci da a kafa wani kwamiti don binciko yadda aka yi tsohon shugaban hukumar cin gashin kan Palastinawan Malam Yasser Arafat ya rasu.
Yayin da yake magana kan labarin da aka yada na cewa an sami wata guba mai halakarwa a jikin tufafin Malam Arafat din, Isma'il Ridhwan daya daga cikin kusoshin kungiyar Hamas din yace wajibi ne a kafa wani bincike don binciko wadanda suke da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa Malam Arafat din yana mai cewa daga dukkan alamu HKI ce ta kashe shi.
Su ma a nasu bangaren, hukumar cin gashin kan Palastinawa ta bakin babban mai shiga tsakani na hukumar Sa'eb Uraikat ya bukaci cibiyoyin kasa da kasa da su dauki wannan batu da muhimmanci sannan kuma su ba da hadin kai wajen gudanar da wannan binciken.
Wata jaridar kasar Faransa ne dai ta fitar da rahoton cewa binciken da aka gudanar kan Arafat din an gano cewa ya mutu ne sakamakon wannan guba ta Polonium da aka sanya masa. Tun da jimawa dai uwargidan Malam Arafat din Suha Arafat ta bayyana cewar lalle an kashe mijin nata ne ta hanyar sanya masa guba tana zargin wasu daga cikin jami'an hukumar cin gashin kan Palastinawa da hannu cikin hakan.
1044901