Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jakarta Post, cewa bangaren kula da harkula da harkokin sadrawa na yankin Jawa a kasar Indonesia tare da kwamitin malaman addinin mulsunci na yankin sun kudiri aniyar cewa za su shiga kafar wando daya da abubuwan da ake watsa a shirin talabijin da radio wadanda suka yi hannun riga da kyawawan dabiu da kuma al’adun mutanen kasar wadda daya ce daga cikin muhimman kasashen musulmi.
Wani labarin kuma ya habarta cewa, yanzu haka ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmin kasar.
1068316