IQNA

Ma’aikatar Kula Da Harkokin Addini A Masar ta Ce A shirye Take Ta Shirya Gasar Kur’ani

17:49 - August 04, 2012
Lambar Labari: 2385256
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addinin mulusnci a kasar Masar ta sanar cewa a halin yanzu a shirye take ta dauki nauyin shirya gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa kamar yadda aka saba a lokutan baya duk kuwa da matsalolin da kasar take fama da su.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram, cewa ma’aikatar kula da harkokin addinin mulusnci a kasar Masar ta sanar cewa a halin yanzu a shirye take ta dauki nauyin shirya gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa kamar yadda aka saba a lokutan baya duk kuwa da matsalolin da kasar take fama da su ta fuskacin tatalin arziki tsaro da sauransu.
Masar dai it ace babbar kasar larabawa da ta bayar da dukaknin gudunmawa ga kasashen yammacin turai da haramtacciyar kasar Isra’ila domin tabbatar da manufofinsu an siyasa da tsaro a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda gwamnatin Saudiyya ta taimaka masu da dukkanin kudaden da suke bukata wajen aiwatar da wannan manufa.
Mai Magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin addinin mulusnci a kasar Masar ya sanar cewa a halin yanzu a shirye take ta dauki nauyin shirya gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa kamar yadda aka saba a lokutan baya duk kuwa da matsalolin da kasar take fama da su a bangarori da dama, tun bayan kifar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar.
1069518
captcha