Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin kasar Amurka ta nun acikakken goyon bayanta bisa ga matakan da Mahukuntan kasar Bahrain suke dauka na murkushe yunkurin da fararen hular kasar suke yin a neman sauyi na demokradiyya a cikin harkokin mulkin kasar wanda bai saba wa ko daya daga cikin kaidojin kasa da kasa ba an kuma kashe su kan haka tare da goyon bayan Amurka.
Kamfanin dilalncin labarin iqn aya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa majalisar dokokin kasar Amurka ta nun acikakken goyon bayanta bisa ga matakan da Mahukuntan kasar Bahrain suke dauka na murkushe yunkurin da fararen hular kasar suke yin a neman sauyi na demokradiyya a cikin harkokin mulkin kasar wanda bai saba wa ko daya daga cikin kaidojin kasa da kasa ba an kuma kashe su kan haka tare da goyon bayan Amurka, da ma wasu daga cikin manyan kasashen yammacin turai da aka shede su da munafunci kamar Birtaniya da faransa.
Wani rahoton kuma dangane da Amurka ya ce sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Cliton ta isa birnin Nairobi na kasar Kenya a yau din nan domin ganawa da hukumomin kasar, wannan kuwa a ci gaba da gudanar da ziyarar aiki ta tsawon kwanaki 11 a nahiyar Afirka. Rahotanni sun ce manyan batutuwan da Cliton za ta fi mayar da hankali a kai a lokacin wannan ziyara a kasar Kenya sun hada da batun zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar a cikin watan Maris na shekara mai kamawa da kuma ganawa da wasu manyan jami'ai na kasar Somaliya mai makwabtaka da kasar.
Wannan ziyara dai ta zo ne kwana daya bayan fashewar wani bam a birnin na Nairobi wanda ake dangantawa da kungiyar Alshabab ta kasar Somaliya wato kasar da Amurkar ta taba mamaye a cikin shekarun baya kafi ta janye dakarunta sakamakon kaskancin da suka fuskanta a kasar.
1071093