IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki Bangaren Salo Na Tartili A Gasar Dubai

14:29 - August 07, 2012
Lambar Labari: 2387823
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a gudanar da bangaren karatun kur’ani mai tsarki bangaren tartil a ci gaba da gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani ta birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar hadadadiyar daular larabawa wanda aka fara gudanarwa tun a cikin makon da ya gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a yau ne za a gudanar da bangaren karatun kur’ani mai tsarki bangaren tartil a ci gaba da gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani ta birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar hadadadiyar daular larabawa wanda aka fara gudanarwa tun a cikin makon da ya gabata kamar dai yadda aka sanr da manema labarai.
Mahaifi kuma wanda ya raka Muhammad Madj makarancin kur’ani dan kasar Iran zuwa gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasawancin hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa akwai karancin masaniya kan yadda ake gudanar da alkalancin gasar kur’ani a matsayi na duniya irin wannan.
A wani labarin na daban kuma yanzu haka dai ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na ashirin a kasar Masar tare da halartar masana daga sassa na kasashen musulmi da na larabawa kamar dai yadda bangaren hulda da jama’a na cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki da kuma shirya gasa.
1072277





captcha