IQNA

An Kafa Wani Gidan Talabijin Na Musulunci A kasar Tunisia Mai Suna Al-Insan

22:42 - August 16, 2012
Lambar Labari: 2394567
Bangaren kasa da kasa, an bude wata tashar talabijin din muslunci akasar Tunisia mai suna Al-insan wadda yanzu haka ta fara watsa shirinta kan tauraron dan adam da nufin gabatr da shiri na muslunci domin amfanin mutanen kasar da kuma bayyana manufofin kungiyar nahdah wadda ke mulki yanzu haka a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bussiness, cewa an bude wata tashar talabijin din muslunci akasar Tunisia mai suna Al-insan wadda yanzu haka ta fara watsa shirinta kan tauraron dan adam da nufin gabatr da shiri na muslunci domin amfanin mutanen kasar da kuma bayyana manufofin kungiyar nahdah wadda ke mulki yanzu haka a kasar da ba ta gama gyagijewa ba.
Wani labarin kuma na daban yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan an nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibviyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor, birnin na boyi ta fuskancin girma da kuma harkokin tattalin arziki na kasar Pakistan.
A wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara. Amma a wannan shekara lamarin ya dauki sabon salo na kara kawata taron.
1079203







captcha