Bangaren kasa da kasa, sayyid Hasan Nasrulalh bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hzibullah a kasar Lebanon zai gabatr da jawabi ga mahalarta taron gawagwarmaya da a za gudanar a birnin Isfahan na jamhuriyar muslunci ta Iran da za a watsa kai tsaye daga ta hanyar manyan allun talabijin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadsarwa na Al-nashrah, cewa sayyid Hasan Nasrulalh bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hzibullah a kasar Lebanon zai gabatr da jawabi ga mahalarta taron gawagwarmaya da a za gudanar a birnin Isfahan na jamhuriyar muslunci ta Iran da za a watsa kai tsaye daga ta hanyar manyan allun talabijin a wurin taron da kuma gidajane talabijin daban-daban.
Kwamitin Zartarwa na Kungiyar 'Yanto Palasdinu ta PLO ya sanar da ranar 20 watan Oktoban wannan shekara a matsayin ranar gudanar da zabuka a duk fadin Palasdinu. A bayan gudanar da zamansa a jiya talata karkashin jagorancin shugaban hukumar cin gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin; Kwamitin Zartarwar Kungiyar 'Yanto Palasdinu ta Palestine Liberation Organization PLO ya tsayar da ranar 20 ga watan Oktoban wannan shekara ta 2012 a matsayin ranar gudanar da zabuka a duk fadin Palasdinu. A karshen zaman taronsa Kwamitin Zartarwar na Kungiyar PLO ya fitar da bayanin cewa: Hukumar Cin Gashin Kan Palasdinawa zata dauki matakin gudanar da zabuka ne kuma a kan ka'idojin zabe mai inganci da aka amince da su.
Har ila yau bayanin Kwamitin Zartarwar na Kungiyar ta PLO ya jaddada cewar bakar siyasar mamaya ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana neman toshe duk wata hanyar kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu, don haka ya zame dole a kan Majalisar Dinkin Duniya ta yi aiki da hakkin da ya a wuyarta na ganin ta amince da Palasdinu a matsayin mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
1091269