Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Info, cewa yahudawan sahyuniya suna kokarin ganin cewa un mamaye sauran yankunan da ke cikin birnin Qods mallakin palastinawa hakan ne ma ya sanya suke kokarin dauke hankulan mutane daga irin tabargazar da suke tafkawa kan al’ummar wannan yanki na gabar yamma da kogin Jordan.
A cikin makon da ya gabata ne aka gudanar da zaman tattaunawa kan ci gaban al’adun Iran da na muslunci a babbar cibiyar bincike da ke gabacin birnin Rom fadar mulkin kasar Italia tare da halartar masana daga kasashen biyu, inda tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi tarihin Iran da kuma n muslunci.
Zaman taron dai ya zo a kokarin da kasashen biyu suke yi wajen ganin sun bude wani sabon shafi ta fuskar bunkasa harkokin al’adu, kasantuwarsu tsoffin dauloli da suka shahara a tarihi tsawon dubban shekaru da suka gabata, wanda kuma suka samu canji a dukaknin bangarori kama daga siysa da kuma akida da al’adu da suke da dangantaka da addinina da suke bi daga bisani bayan samun sauyi a cikin tafiyarsu.
An gudanar da zaman tattaunawa kan ci gaban al’adun Iran da na muslunci a babbar cibiyar bincike da ke gabacin birnin Rom fadar mulkin kasar Italia tare da halartar masana daga kasashen biyu wadanda suka gabatar da laccoci da kuma kasidu da suka shirya domin zaman taron.
1091485