IQNA

20:30 - September 17, 2012
Lambar Labari: 2413673
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a kasar masar ta hukunta wani saurayi day a yi cin zarafi ga addinin muslunci a kasar ta hanyar bayyana a ddinin mulunci amtasayin wani addini maras ci gaba da koma baya acikin dukaknin lamurra na rayuwa lamarin day a fuskanci fushin mutanen kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar uam sabi, cewa wata kotu a kasar masar ta hukunta wani saurayi day a yi cin zarafi ga addinin muslunci a kasar ta hanyar bayyana a ddinin mulunci amtasayin wani addini maras ci gaba da koma baya acikin dukaknin lamurra na rayuwa lamarin day a fuskanci fushin mutanen kasar wadda ake buga misali da ita.
Al'ummomin musulmi na ci gaba da gudanar da gangami da jerin gwano a kasashe daban-daban na duniya, domin yin Allawadai da kakakusar murya kan fitar da fim din batunci ga addinin musulunci da aka yi a kasar Amurka. Fim din wanda masu tsananin adawa da addinin muslunci suka shirya a kasar Amurka, yana nuna musulmi a matsayin wasu mutane masu kama dabbobi da babu 'yan adamtaka tare da su, tare da bayyana su a matsayin wasu 'yan ta'adda da manzon Allah Muhammad (SAW) yake jagoranta domin aiawatar da wannan ta'addanci. Wannan lamari ya harzuka miliyoyin al'ummar musulmi a ko'ina cikin fadin duniya, inda a wasu wurare wasu musulmi suka dauki matakin mayar da martani kan gwamnatin Amurka, wadda ta bayar da damar yin hakan a cikin kasarta da sunan 'yancin bayyana ra'ayi ko fadar albarkacin baki, inda a kasar Libya dubban mutanen suka yi zanga-zanga domin la'antar gwamnatin Amurka, kuma suka nufi ofisoshin jakadancinta da ke birnin Bengazi, amma sojojin Amurka da suke gadin wurin sun yi harbi da bindiga kan masu zanga-zangar, lamarin day a jawo mummunar hatsaniyar da ta kai ga hallaka jakadan Amurka da wani jami'in dilplomasiya gami da wasu sojojin Amurka biyu. Wannan dai ya bakanta wa Amurka matuka, musamman ma ganin cewa hakan ya faru bayan kafa gwamnati ne da ke kare manufofinsu a kasar, lamarin da ke tabbatar da cewa kashe Gaddafi ba lamuni ne ga Amurka ba domin ta ci karenta babu babbaka a kasar Libya kamar yadda ta yi tsammani. A kasar Masar ma dubban mutane sun afka kan ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Alkahira, inda suka safkar da tutar Amurka suka banka mata wuta domin nuna fushinsu da rashin amincewarsu da cin zarafin manzon Allah da addinin muslunci da ake yi a kasar Amurka, an gudanar da irin wannan jerin gwano a kasashen Sudan, Iraki, Afghanistan, Iran, Pakistan, Morocco, Murtaniya, Yeman Tunisia, duk kuwa da cewa jami'an tsaron kasar Tunisia sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake domin tarwatsa masu zanga-zangar. Gwamnatocin kasashen Sudan, Iran, Pakistan da Afghanistan sun fito karara sun Allawadai da wannan mummunan aiki, kamar yaddad fadar Vatican ita ma ta fito ta yi Allawadai da hakan, tare da bayyana cewa keta alfarmar ababe masu tsarki na addinin muslunci ba koyarwar addinin kirita ba ne, yayin das u kuma gwamnatocin Masar da Libya suka baiwa Amurka hakuri kana bin da ya faru da ofisoshin jakadancinsu a kasashensu, da kuma kashe jakadanta da aka yi a Libya. A cikin wani bayani da kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ta fitar, ta yi ishara da cewa fitar da wannan fim na batunci ga manzon Allah da aka yi a kasar Amurka, ya nuna irin tsananin gabar da ake yi da addinin muslunci a wannan kasa, wanda kuma hakan sakamako ne na siyasar da gwamnatin kasar ta shimfida kuma ta tora mutanen kasar a kai. Bayanin na kungiyar Hizbullah ya ce idan har haka ta faru a Amurka ba abin mamaki ba ne, amma abin mamaki da ban takaici shi ne yadda kasashen da ke tinkaho da cewa su ne jagororin musulmi a duniya, su ne kuma a lokaci guda manyan kawayen Amurka da ke kare bakaken manufofinta na siyasa kan sauran kasashen msuulmi da na larabawa. Bayanin ya ce ina kungiyar hadin kan kasashen larabawa? Ina kungiyar kasashen musulmi? Ina manyan kasashen larabawa? Me gwamnatocinsu suka yi kan wannan cin zarafi da aka yi wa manzon Allah da addinin muslunci? A maimakon haka ma suna ta yin amfani da biliyoyin kudin da suke samu na man fetur da suke sayarwa ne domin ganin sun kare manufofin siyasar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin gabas ta tsakiya
1099504
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: