Bangaren kasa da kasa, mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmayr hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa batuncin da makiya suke yi ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka wata alama ce ta gazawa daga makiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa Sheikh Naim Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmayr hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa batuncin da makiya suke yi ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka wata alama ce ta gazawa daga makiya addinin muslunci.
A wani labarin kuma jiragen yakin ruwa guda biyu mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun karasa zuwa tashan jiragen ruwa Tatus da ke kasar Syrai a yau Asabar. A yau din ne jiragen biyu suka tsallaka mashigar ruwa ta Swiz a kasar Masar suka fada cikin tekun Medeteranina, wannan dai shi ne karo na biyu a wannan shekarar wanda jiragen ruwan yaki na kasar Iran suke tsallakawa zuwa tekun Medeteranian.
Rear Admiral Habibullah Sayyari ya fadawa gidan television na PressTv wanda ke watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran cewa, manufar zuwan wadan nan jiragen ruwa shi ne bawa sojojin kasar Syria horo bisa yerjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.
Sayyari ya kara da cewa shigar Jiragen ruwan yakin kasar Iran yankin Medeterianian har'ila yau yana nuna irin karfin sojen da kasar take da shi da kuma isar da sakon zaman lafiya ga kasashen yankin.
1106047