IQNA

Saudiyya Na Yin Amfani Da ‘Yan salafiyya Wajen Fuskantar Yan Shia Da Ikhwan

8:03 - October 01, 2012
Lambar Labari: 2423181
Bnagaren kasa da kasa, gwamnatin wahabiyawan Saudiyya na yin amfani da yan salafiyya wajen kalu balantar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da kuma yan ikhwan a cikin kasashen da aka samu sauyi da kuma wuraren da ta haddasa rikici a halin yanzu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga cikin shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa gwamnatin wahabiyawan Saudiyya na yin amfani da yan salafiyya wajen kalu balantar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da kuma yan ikhwan a cikin kasashen da aka samu sauyi da kuma wuraren da ta haddasa rikici a halin yanzu kamar Syria da sauransu.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawan sahyuniya.
1109192






















captcha