IQNA

UNESCO Ta Yi Kira Da Sauki Matakan Hana Wulakanta abubuwa Masu Tsarki Na Addinai

17:02 - October 10, 2012
Lambar Labari: 2429541
Bangaren kasa da kasa, kungiyar UNESCO ta yi kira da a dauki matakai na kasa da kasa domin hana cin zarafin da wulakanta abubuwa masu tsarkia cikin sauran addinai musamman ganin cewa hakan na karuwa matuka a yanzu a cikin kasashne yammacin turai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa kungiyar UNESCO ta yi kira da a dauki matakai na kasa da kasa domin hana cin zarafin da wulakanta abubuwa masu tsarkia cikin sauran addinai musamman ganin cewa hakan na karuwa matuka a yanzu a cikin kasashne yammacin turai da wasu kasashen Asia.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Rasha ta sanar a yau talata cewa ta kulla yarjejeniyar cinikin makamai na kimanin dalar Amurka milyan dubu 4 da milyan dari 2 da kasar Iraki, wanda ya bai wa Rashar damar kasancewa kasa ta biyu mafi muhimmanci a wajen sayar wa Irakin da makamai baya ga kasar Amurka. Kamfanin dillacin labarai na kasar ta Rasha ya bayyana cewa tawagar Firayi ministan Iraki Nuri Al-maliki da ke gudanar da ziyara a kasar, ita ce ta sanya hannu kan cinikin makaman da kuma sayen wasu muhimman abubuwa da Irakin ke bukata daga Rasha.
Da farko dai wata jaridar kasar ta Rasha mai suna Vedomosti, ta rubuta labarin cewa daga cikin makaman da Irakin ta saya sun hada da wasu jiragen yaki guda 30 kirar Mi-28 da Mi-42 da kuma wasu makamai masu linzame da ake harbawa daga kasa zuwa sama kirar Pantir- a lokacin wannan ziyara da Firayi minista Maliki ya soma a jiya litinin, ya samu ganawa da Firayi ministan Rasha Dmitri Medvedev kafin daga bisani ya gana da shugaba Vladamir Putin.
Manazarta dai na kallon wannan ziyara ta Nuri Al-maliki a kasar Iraki a matsayin wani koma-baya ga kasar Amurka wacce ke ci gaba da yin kane-kane kan duk wasu al'amurra da na tsaro da kasuwanci a kasar ta Iraki tun bayan faduwar gwamnatin Saddam Hussein.
1117032


captcha