IQNA

malamin nan na Iran Allamah Hakim Qudbudden Shirazi da aka gudanar a garin Shiraz da ke kudancin kasar Iran.

15:55 - December 27, 2012
Lambar Labari: 2471053
An bude taron ne da karon sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa mahalarta taron wanda Ayatullah Imani, wanda wakilin Jagora a lardin Fars kuma limamin juma’ar garin Shiraz ya karanto.
A cikin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wajibcin sake dubi cikin zamanin ci gaban ilimi na Iran da kuma gabatar da rayuwar fitattun mutanen da suka yi fice a fagen ilimi na kasar a matsayin abin koyi ga matasan yau. Jagoran ya ci gaba da cewa: sakamakon samuwar wadannan fitattun mutanen a matsayin abin koyi, don haka babu bukatar sai an tono wasu mutane da suka yi rayuwa a lokacin jahiliyyar kasashen Turai da kuma gabatar da su a matsayin abin koyi.

Har ila yau Jagoran ya ce girmama mutane irin Qudbuddeen Shirazi aiki ne mai amfani don matasanmu na yau su san cewa suna da wasu mutane wadanda za su sanya su zamanto musu abin koyi.

Har ila yau Jagoran ya ce ilimi dai ya samu gagarumar daukaka a Iran tun ma kafin a lokacin da kasashen Turai suke cikin bakin duhun jahilci.

Shi dai Allamah Qudbuddeen Shirazi daya ne daga cikin masanan kasar Iran na karshe-karshen karni na bakwai da kuma farko-farkon karni na takwas hijiriyya wanda aka haiffe shi a shekara ta 633 sannan kuma ya rasu ne a shekara ta 710 hijiriyya. Sannan kuma ya taka gagarumar rawa wajen yada hikima da falsafa da ilimin likitanci da sauransu.

captcha