IQNA

Kisan Kiyashin Da Ake Yi Kan 'yan Shi'a A Pakistan Aikin wahabiyawa Ne

23:26 - January 15, 2013
Lambar Labari: 2480951
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masana a kasar Pakistan sun bayyana cewa kisan kiyashin da ake yi kan mabiya tafarkin iyalan gidan anzon Allah a kasar at Pakistan yana daga cikin ayyukan mabiya tafarkin wahabiyanci a kasar domin kuwa al'ummar Pakistan bas u san da wani abu mai kama da haka ba a lokutan baya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo tashar talabijin din press TV cewa, da dama daga cikin masana a kasar Pakistan sun bayyana cewa kisan kiyashin da ake yi kan mabiya tafarkin iyalan gidan anzon Allah a kasar at Pakistan yana daga cikin ayyukan mabiya tafarkin wahabiyanci a kasar domin kuwa al'ummar Pakistan bas u san da wani abu mai kama da haka ba.
Al-ummar shia a jihar Buluchistan na kasar Pakistan ta amince ta bisne kawakin mamatanta sanadiyyar wasu hare haren boma bomai da aka kaimata a ranar Alhamis da ta gabata bayan ganawarsu da priministan kasar a jiya. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa bayan ganawa da Priminista Rajah Parviz Asharaf, al-umma shia a jihar Buluchistan zata kawo karshen zaman dirshen da ta yi da gawakin mamatanta 110 na tsawon kwanaki ukku.
Priministan bayan ganawa da shuwagabannin yan shia a yankin ya amince ya kauda gwamnatin jihar da kuma maye gurbin wasu jami'an gwamnatin yankin wadanda al-ummar shia take zargim da cewa suna da hannu cikin hare haren da ake kaimata a yankin. Wata kunhiyar yan ta'adda mai suna Lashkar c eta dauki nauyin kai hare hare kan al-ummar shia jihar buluchistan na kasar Pakistan a ranar alhamis da ta gabat wanda ya kashe mutane 110 ya kuma raunata wasu 200.

1171227



captcha