Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani bayani da a ciki ta ja kunnen gwamnatin Myanmar akan kisan da ake yi wa musulmin kasar. A bisa rahoton da kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto, Shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya ya yi gargadi mai karfi akan yadda ake fakewa da rikicin kabilanci a kasar domin korar tsirarun musulmin da ake da su.
A cikin fadan bayan nan a yankin Rakhin da ke yammacin kasar an kashe abinda bai kasa musulmi 300 ba. Dan rahoton musamman na majalisar dinkin duniya akan kasar Myanmar Tomas Ojna Koyantata ya ce: "Abinda ya ke faruwa wani shiri ne da tsari domin shafe tsirarun da ake da shi a cikin al'umma." Bayanin ya kuma nuna damuwarsa akan yadda gwamnatin Mayanmar ta bayyana musulmin kasar da cewa: "Yan gudun hijira ne ba bisa doka ba.
Har ila yau ya ci gaba da cewa; Matukar kasar da ta ke son hawan turbar demokradiyya tana son samun dace, to dole ne ta zama mai jarunta wajen warware matsalolin take hakkin bil'adama.
1199621