IQNA

Mata A Iran Sun Taka Rawa Wajen Bude Sabon Shafin Tarihi Ga Sauran Mata Na Duniya

9:38 - March 07, 2013
Lambar Labari: 2507578
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga taron kara wa juna sani na mata shahidai da aka bude a birnin Tehran, wanda yake samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto cikakken bayanin daga shafin jagora da ke cewa, Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, A yau kun taru a nan ne don girmama dubban mata shahidai wadanda suka taka gagarumar rawar da ta dace wajen sauya tafarkin tarihin Musulunci da kuma kasar nan sannan kuma suka koma wajen Allah Madaukakin Sarki cikin girma da daukaka. Ko shakka babu wadannan dakaru wadanda suka sadaukar da rayukansu masu tsarki a tafarkin Musulunci, ba su kasance 'yan kallo ba, sun shigo cikin fagen aiki da kuma taka gagarumar rawa wajen gina sabuwar kasar Iran. Sun kasance mataye masu girma da suka gabatar wa kasashen yammaci da sabuwar ma'anar kalmar mace.
Mace dai a mahangar kasashen gabashi tana a matsayin wata halitta ce da aka ajiye ta a gefe wacce ba ta da wata rawa da za ta taka wajen gina tarihi; a yammaci kuwa tana a matsayin wata halitta ce wacce jinsinta yake sama da matsayinta na 'yar'adam sannan kuma (tana a matsayin) wani kayan aiki ne na biyan sha'awar namiji sannan kuma haja ga 'yan jari hujja. Jaruman matan wannan juyi da kuma kallafaffen yaki sun tabbatar wa duniya cewa akwai wata abar koyi ta daban ga mata, wadda ta saba wa mahangar gabashi da yammaci kan mace. Mata musulmi na Iran sun bude wa matan duniya wani sabon shafi na tarihi, sannan kuma sun tabbatar musu da cewa mace tana iya zama a fage alhali kuma tana mai kiyaye mutumcinta da hijabinta da kuma daukakar da take da ita. Za a iya kiyaye nauyin gudanar da iyali cikin tsarki da kyawawan halaye a daidai lokacin da kuma ake cikin fage na siyasa da zamantakewa sannan kuma a sami nasarori masu yawa. Wadannan mata sun iya hada irin tausayi da rahama ta mace tare da ruhi na jihadi da shahada da gwagwarmaya, sannan kuma suka iya samun nasara a fagage irin na maza cikin jaruntaka da ikhlasi da sadaukarwa.
A lokacin juyin juya halin Musulunci da kuma kallafaffen yaki, an sami wasu mata da suka shigo cikin fage sannan suka bayyanar wa duniya ma'anar mace da kasantuwarta a fagagen ci gaba da tsarkake zuciya, da fagagen kiyaye gida da iyali cikin ingantacciyar hanya, haka nan kuma a fagen na zamantakewa da jihadin umurni da kyawawan aiki da hani da munana da kuma jihadi na zamantakewa, sannan kuma suka kawo karshen gagarumar tsaka mai wuyan da ake ciki a wadannan fagage.
A halin yanzu, albarkacin jinin wadannan mataye, a wannan zamani na mu an samu bayyanar sabon tsayin daka wanda kuma ya fara yin tasirinsa a duniyar musulmi, sannan kuma a nan gaba ko ba dade ko ba jima zai taka gagarumar rawa wajen tabbatar da makoma da kuma matsayin mata a duniya. Albarkacin hasken Khadijatul Kubra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) da Fatima al-Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) da kuma Zainabul Kubra (amincin Allah ya tabbata a gar eta), ko shakka babu tsohon da sabon shirin 'fada da mace' ba zai kai ga nasara ba. Sannan kuma dubban matanmu masu akidar Karbala, ba wai kawai sun sami damar ruguza mummunan tafarkin zalunci na zahiri ba ne, face ma dai sun kwance wa zalunci na zamani da ake yi wa mace zani a kasuwa, da kuma tabbatar da cewa karamar da Ubangiji ya ba wa mace, ita ce mafi girman hakkin mace wanda a irin wannan duniya da ake kiranta na zamani ba a girmama shi. To yau dai lokaci ne na girmama hakan.
Ina taya iyalan wadannan shahidai masu girman matsayi murna sannan kuma ina fatan albarkacin jinin wadannan mataye masu girma da daukaka kuma majahidai kafafen watsa labarai da masu shirya fina-finai da sauransu za su sami damar isar da wannan jihadi mai girma da matan Iran musulmi suka yi ga duniya wacce take bukatar sanin irin wadannan abubuwa.
Mata musulmi na Iran za su zamanto malamai na biyu ga matan duniya, bayan malaman farko wadanda su ne mata mujahidai na farkon Musulunci.
Amincin Allah ya tabbata ga Madaukakiyar macen Musulunci mai girma Nana Fatima al-Zahra da kuma dukkanin matan farkon Musulunci masu girma haka nan kuma ga mata masu sadaukarwa na kasar Musulunci ta Iran.
Sayyid Ali Khamenei
15, Esfand, 1391
(05, Maris, 2012)

1200280

captcha