IQNA

An ba shugaban kasar Masar sa'oi 48 domin gano wadanda suka kashe Sehhata

14:01 - June 29, 2013
Lambar Labari: 2553471
Bangaren kasa da kasa, almajiran Sheikh Hassan Shehhata da suka hada da lauyoyi da kuma malaman jami'a da likitoci da 'yan jarida, suka kira wani taron manema labarai a birnin Alkahira, inda suka bai wa shugaban kasar ta Masar Muhammad Morsi wa'adin sa'o'i 48 da ya gano dukkanin wadanda suke da hannu wajen yi wa malamin kisan gilla, idan kuma ba haka ba, to za su shigar da kara a kotun manyan laifuka ta duniya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, dazu-dazun nan ne wasu daga cikin almajiran Sheikh Hassan Shehhata da suka hada da lauyoyi da kuma malaman jami'a da likitoci da 'yan jarida, suka kira wani taron manema labarai a birnin Alkahira, inda suka bai wa shugaban kasar ta Masar Muhammad Morsi wa'adin sa'o'i 48 da ya gano dukkanin wadanda suke da hannu wajen yi wa malamin kisan gilla, idan kuma ba haka ba, to za su shigar da kara a kotun manyan laifuka ta duniya a kan gwamnatin Masar.

Rikicin na Masar dai ya kara kamari ne biyo bayan jawabin da shugaban kasar Muhammad Morsi ya gabatar a Larabar da ta gabata, inda ya dora alhakin dukkanin abin da yake faruwa na tashe-tashen hankula a kasar a kan bangarorin siyasa da suke adawa da shi, inda ya kira da mabarnata, tare da shan alawashin shiga kafar wando guda da su, duk kuwa da cewa daga bisani a cikin bayaninsa nasa ya kiraye su zuwa ga tattaunawa, amma bangarorin adawar sun yi watsi da wannan tayi nasa, tare da bayyana hakan a matsayin wani shure-shure ne da Morsi ke yi, domin kuwa a cewarsu a gobe Lahadi za su gudanar da wata zanga-zanga mafi girma a kasar, wadda za ta kai ga kifar da gwamnatinsa, daga bayan gabatar da jawabin Morsia daren Laraba zuwa safiyar yau Asabar, mutane 7 ne suka rasa rayukansu, wasu fiye da 500 kuma suka samu raunuka sakamakon rikicin da ya biyo bayan jawabin nasa.

Ko shakka babu abin da yake faruwa a kasar ta Masar a halin yanzu ba bushara ce ta alkhari ga makomar kasar ba, musamman ma idan aka yi la'akari da yadda 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma wasu daga cikin 'yan salafiyya na kasar suka tsaya kai da fata tare da gindaya rayuwarsu a kan cewa ba za su taba amincewa da duk wani mulki in ban a Morsi ba, a daya bangaren kuma masu adawa da magoya bayansu suka tsaya kai da fata a kan cewa dole sai Morsi ya safka domin gudanar da wani zabe na gaggawa, kuma ga dukkanin alamu ba daya daga cikin bangarorin biyu da yake shirye domin yin sassuci kan matsayinsa.

1248985
captcha