IQNA

Ana ci gaba da taho mu gama tsakanin mago bayan Morsi da kuma masu adawa

17:46 - July 23, 2013
Lambar Labari: 2566006
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Masar na nuni da cewa ana ci gaba da taho mu gama tsakanin 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma masu adawa da hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar ta rubuta a shafinta na yanar gizo a 'yan sa'oin da suka gabata cewa, tun a yammcin jiya ake dauki ba dadi tsakanin magoya bayan Morsi da kuma masu adawa da shi a cikin birnin Alkahira da kuma wasu biranan kasar.

Rahoton ya ce wasu daga cikin magoya bayan Morso sun kawo farmaki kan masu zaman dirshan a dandalin Tahrir a daren jiya da suke neman a hukunta Morsi, inda suka yi ba ta kashi mai tsanani, amma daga bisani maharani sun jaye zuwa masallacin Rabi'at Adwiyyah inda suke zaman dirshan domin neman a dawo da Muhammad Mursi kan kujerar shugabancin kasar.

Akalla mutane 3 aka tabbatar sun rasa rayukansu daga yammacin jiya zuwa safiyar yau, yayin da wasu daruruwa kuma suka jikkata, wani bayanin kuma ya ce adadin yah aura hakan.

Rikici tsakanin magoya bayan hanbararren shugaban kasar Masar Muhamad Mursi da ‘yan adawarsa ya janyo asarar rayukan Mutane 2 tare da raunuka wasu mutane 7. Gidan Telvijin na kasar Masar ya habarta cewa rikicin da ya faru a jiya litinin tsakanin ‘yan adawa da magoya bayan hanbararren shugaban kasar Muhamad Mursi a kusa da dandalin Tahrir na birnin Alkahira ya janyo asarar rayukan mutane 2 tare da jikkata wasu 7 na daban.

Wadanda suka ganewa idanunsu abunda ya wakana sun bayyana cewa bangarorin biyu sun riga jifan junansu da duwatsuna tare da kwalabe bayan daga bisani jam’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa don shiga tsakaninsu.

1262033








captcha