IQNA

Mutanen Syria Sun Soki Lamirin Zaman Kasashe Masu taimakon ‘Yan ta’adda

23:04 - October 23, 2013
Lambar Labari: 2607875
Bangaren kasa da kasa, Ministocin harkokin wajen kasashe abokan ‘yan tawayen Syria sun gudanar da zaman taro a jiya a birnin London na kasar Birtaniya, inda suka tattauna kan batun taron Geneva, wanda ake sa ran gudanarwa a cikin watan Satumba mai kamawa domin samo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Syria.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Kasashen 11 dai su ne Amurka, Faransa, Birtaniya, Jamus, Saudiyya, UAE, Turkiya, Masar, Qatar, Italiya da kuma Jordan, gami da shugaban majalisar ‘yan tawayen kasar ta Syria Ahmad Jarba. Dukkanin kasashen dai sun jaddada wajabcin halartar bangaren ‘yan adawa da suke mara wa baya, domin samun hanya guda wadda za a bi domin kawo karshen rikicin.
A wannan karon dai kalmomin da aka saba ji daga bakunan jami’an wadannan kasashe sun banbanta da na sauran lokutan baya, domin a wannan karon manyan kasashe daga cikinsu musamman Amurka da Faransa da kuma Birtaniya, sun jaddada cewa babu wata hanya ta kawo karshen rikicin Syria illa komawa kan teburin tattaunawa tare da yin sulhu tsakanin bangarorin rikicin, sabanin lokutan baya da suke kira da a aike da makamai ga ‘yan bindiga domin kifar da gwamnatin shugaba Bashar Assad.
Wannan canjin matsayi na zahiri daga manyan kasashen turai dangane da rikicin Syria musamman ma Amurka ya bakanta wa mahukuntan kasar Saudiyya matuka kamar yadda jaridar Journal Wall Street ta kasar Amurka ta fada, inda jaridar ta ce shugaban hukumar leken asirin kasar Saudiyya Bandar Bin Sultan ya sheda wa wasu daga cikin jami’an diplomasiyya na kasashen turai cewa, Saudiyya za ta rage karfin dangantakarta da Amurka, saboda sassaucin da Amurka take nuna a halin yanzu akan batun Syria da kuma Iran.
A nasa bangaren sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a lokacin da yake bayar da amsa dangane da wannan batu a birnin London, ya bayyana cewa hakika mahukuntan Saudiyya sun nuna matukar damuwarsu sakamakon dakatar da kai harin soji kan kasar ta Syria da Amurka ta shirya yi, amma wannan ba zai tasiri a alakar tarihi da ke tsakanin gwamnatocin Amurka da Saudiyya ba.
1307068
captcha