IQNA

Mutane Na Nuna Goyon Bayansu Ga Musulmi Da Ake Cima Zarafi A Kasar Australia

23:01 - November 24, 2014
Lambar Labari: 2611419
Bangaren kasa da kasa, cincirindon mutane sun fito suna nuna goyon bayansu ga musulmi da ake ci wa mutunci a wasu yankuna na kasar Australia saboda kiyayya da addininsu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ABC NEWS cewa, Victoria Martin daya daga cikin mutane suka fito domin nuna goyon bayansu ga musulmi da ake ci wa mutunci a Australia ya bayyana cewa, su makwaftanmu ne babu dalilin da zai sanya a rika muzgunamusu.
A can kasar Canada ma Majalisar da ke kula da harkokin al’ummar musulmin kasar  ta sanar da cewar mabiya addinin Musulunci a kasar suna fuskantar matsananciyar tsangwama da cutarwa, majalisar ta al’ummar musulmin kasar  a jiya Alhamis ta sanar da cewa; Tun bayan harin wuce gona da iri da wani mutum mai suna Zehaf-Bibeau ya kai kusa da harabar Majalisar  dokokin kasar a ranar ashirin da biyu  ga wannan wata na ktoba lamarin da ya kai ga kisar sojin kasar, alummar musulmin suka kara fuskantar matsin lamba, cin zarafi, musgunawa da kuma kara fuskantar barazana daga jama’a, musamman a wajajen taruwan mutane ko a cikin ababan hawa ta haya gami da rubuce-rubucen batanci ga addinin Musulunci har a jikin gilasan motoci.
Rahotonni daga kasar suna bayyana cewar an samu ninkin irin cin zarafi da musgunawan da ake yi ga musulmi a kasar har sau goma sakamakon harin ta’addancin makon da ya gabata. Mahukuntan kasar dai sun yi da’awar cewa Zehaf-Bibeau ya musulunta ne a shekara ta 2004 kuma dan kungiyar ta’adanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham ne wato desh.

2611151

Abubuwan Da Ya Shafa: australia
captcha