Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-youm Sabi cewa a cikin kwanakin nan cibiyar addinin muslunci a kasar Masar ta Azhar na shirin daukar nauyin gudanar da wani zaman taro a kasar wanda zai yi dubi kan hanyoyin day a kamata a bi domin yaki da mummunar akidar kafirta musulmi da ke haddasa ta'addanci a duniya.
A nasa bangaren shugaban Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar da kuma Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa sun jaddada wajibcin yaki da akidun wuce gona da iri wadanda suke bata fuskar addinin musulunci a kasashen larabwa.
Wannan kamfanin dillancin labarai ya nakalto shugaban Jami'an Al-Azhar da kuma babban sakataren kungiyar kasashen larbawa wadanda suka gana a taron ministocin harkokin waje na kasashen larabawa wanda ake gudanar a birnin Alkahira suna fadar haka a jiya.
Shugaban jami'ar ya ce Jami'ar Al-Azhar za ta yi yaki da wadannan mummunan ikidu ta hanyar yada akidun musulunci na gaskiya da kuma bude fagen muhawara da jawabai don kushe dukkan akidu masu munana fuskar addinin musulunci a kasashen larabawa da ma sauran kasashen musulmi.
Shi ma a nashi bangaren shugaban kungiyar kasashen larabawa ya jaddada muhimmancin Jami'ar Al-Azhar a matsayinta na cibiyar ta yada addinin musulunci, wajen yakar yan ta'adda da kuma mummunan akidun da wasu ke dangantasu da addinin musuluni a duniya a wannan zamani.
2613560