IQNA

Yin Koyi Da Manyan malamai Shi Ne Hanyar Yaki Da 'Yan Ta'addan Takfiriyyah

22:47 - December 13, 2014
Lambar Labari: 2617906
Bangaren kasa da kasa, shugaban majlaisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar hanyar yaki da 'yan ta'adda masu dauke da akidar takfiyya it ace yin koyi da manayan malamai na gari na shi'a da kuma sunnah a tsakanin dukkanin musulmi.

Kmafanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-safir ta kasar Lebanon cewa, Nabi Birri shugaban majlaisar dokokin kasar ya bayyana cewa,a  irin wannan yanayi da ake ciki, babbar hanyar yaki da 'yan ta'adda masu dauke da akidar takfiyya ta kafirta musulmi, ita ce yin koyi da manayan malamai na gari na shi'a da kuma sunnah a tsakanin dukkanin musulmi na duniya baki daya.
Akasarin al'ummomin kasashen da ke fama da matsalar dai suna ganin cewa babu wani abin a zo a gani da wannan kawance kasashen yamam ya tabuka ba wajen murkushe 'yan ta'addan  a cikin kasashensu, illa dai kawai sojojin wadannan kasashe ne da kuma masu shiga aikin sojin sa kai ne kawai suke yin iyakacin kokarinsu wajen yaki da wadannan 'yan ta'adda, yayin da wasu ke ganin cewa lamarin ya yi kama da wasan kwaikwayo.
Idan aka yi la'akari da cewa kasashen da suka kirkiro wadannan 'yan ta'adda kuma suka horar da su musamman ma ita kanta jagorar kawancen da wasu kasashen turai, tare da 'yan koransu daga cikin larabawa musamman ma dai saudi a daya bangaren, wadanda suke kwaso su daga kasashen duniya zuwa wadannan kasashe da sunan jihadi, tare da ba su muggan makamai da makudan kudade, su ne kuma a lokaci guda a cikin wannan kawance na yaki da wadannan 'yan ta'adda da suka kafa.
Hakan ya sanya wasu masu bin diddigin abubuwan da ke wakana yin imanin cewa, babbar manufar wadannan kasashe ba ita ce yaki da kungiyar 'yan ta'addan na daesh ko murkushe ba, domin su ne suka kafa su kuma su ne suka fi kowa saninsu da hanyar da za su iya murkushe su, masu wanann ra'ayin na ganin cewa manufar ita ce rusa kasashen larabawa da na musulmi.
2617724

Abubuwan Da Ya Shafa: Birri
captcha