IQNA

Jami’an Tsaron Kasar Bahrain Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Masu Adawa

16:56 - December 27, 2014
Lambar Labari: 2636271
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Bahrain na ci gaba da kaddamar da harin zalunci kan fararen hula masu adawa da salon mulkin kama karya da danniya na masarautar kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, Nabil Rajab jagoran gwagwarmaya da kare hakkin bil adama a Bahrain ya bayya acewa jami’an tsaron kasar ta Bahrain na ci gaba da kaddamar da harin zalunci kan fararen hula masu adawa da salon mulkin kama karya da danniya na masarautar Al khalifah.
Al'ummar kasar Bahrain sun gudanar da zanga-zanga a jiya juma'a don nuna Adawarta da Milkin kama karya na Gwamnatin Ali khalifa.   Dubu dubatar Al'ummar Bahrain ne suka bazu a kan titunan baban birnin kasar a jiya juma'a bayan gama Sallar juma'a don nuna adawarsu da irin milkin kama karya da Gwamnati Ali khalifa ke yi masu.
Mahalarta zanga-zangar na rera takan cewa yayi masu tsari da zalinci sannan sun bayyana da gogormawa har sai sunga karshen milkin zalinci a kasar.
Daga bangare guda kungiyar Matasa na goma sha hudu ga watan Fabrairu sun yi a..wadai kan yadda 'yan sanda suka bugi uwar shahararen dan siyasar nan Kais Abbasi sannan sun bukaci dukkanin 'yan siyasar kasar suka matsa lamba kan Gwamnatin kasar don ganin an kawo karshen zalinci a kasar.
Yayin kama Kais Abas ma'aifiyarsa ta nuna adawarta wanda hakan ya janyo ta fuskanci duka daga jami'an 'yan sanda na kasar ta Baharain inda aka ce har ma sun jikkata ta, bayan kama Kais Abbas kotu ta yanke masa hukunci shekaru goma a gidan kaso.
Tun  a shekara ta dubu biyu da sha daya Al'ummar kasar ta Bahrain ta fara gudanar da zanga-zangar lumana don nemam Gwamnatin ta gudanar da sauye-sauye a kasar inda Gwamnatin ta Ali Khalifa tayi kunnan uwar sheku da bukatun Al'ummar kasar  sannan ta zabi amfani da karfi wajen murkushesu,wanda hakan ya janyo kisan kimanin Mutane dari da arbain tare da jikkata dariruwan Mutanan kasar.
2634868

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha