Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Salahudin Mazwar ministan harkokin wajen kasar Morocco ya ce yaki halartar gangamin Paris ne saboda an daga wasu zane-zanen batunci da cin zarafi ga manzon Allah da addinin muslunci da aka yi a wurin.
An kawo karshen taron gangamin hadin kai da aka shirya a marecen yau lahadi da nufin yin tir da Allah-wadai da harin ta'addancin da aka kai a kasar wanda ya hada dana farfajiyyar jaridar barkwancin nan ta Charlie Hebdo.
Gangamin ya samu hallartar shugabanin kasashe kusan hamsin da milyoyin mutane daga sassa daban-daban na kasar inda akayi shiri na minti tareda tataki na dan locaci domin nuna alhini da yin tir da harin ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a birnin Paris wanan ya hadasa mutuwar mutane 17 da kuma maharan uku.
A wani hadin kai da ba'a shirya masa ba, shugabannin Isra'ila da Falasdinawa na daga cikin wadanda suka halarci wannan gangami tare da takwarorinsu na sauran kasashe bisa kasashe. Daga cikin shugabannin kasashen Afrika da suka amshi goron gayatar takwanran su na Faransa.
Matakin da ministan harkokin wajen kasar ta Morocco ya dauka ya zama abin yaboa wajen wasu da suke ganin cewa akwai siyasa cikin wannan lamari, kuma manufar hakan it ace kara bakanta fuskar addinin muslunci a wyen al’ummomi na kasashen yammacin turai.
2698570