Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Mail cewa, Lasana Bathily matashi musulmi dan shekaru 24 da haihuwa a lokacin da aka kai hari kan wani babban shagon sayar da kaya na yahudawa a birnin Paris wannan matashi ya tseratar da masu sayayya a cikin wanann shago.
Bathily ya ce a lokacin da ‘yan ta’addan suka shigo dauke da makamai, yay a kashe wuta a bangaren da yake, kuma ya umarci wadanda suke wurin da su yi shiri kada su ce uffan, da hakan ya samu nasarar tseratar da mutane kimanin 15 daga cikin wadanda ke wurin.
Shi ma a nasa bangaren Malik Zaidi wani matashi musulmi dan shekaru 25 da ke sayayya a wurin ya sheda wa jaridar Washington Post cewa, wannan wuri ya zame musu wurin ciniki, domin kuwa ba yahudawa kawai ba har ma musulmi da kiristoci duk suna sayen kaya a wurin ba tare da wata matsala ba..
A sanarwar da kungiyar musulmin kasar Faransa ta fitar a yau Litinin ta bayyana cewar tun daga lokacin da wasu matasa suka kai hari kan gidan jaridar Charlie Hebdo da ta yi zane-zanen batanci da cin zarafi ga Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}, inda suka halaka ma’aikatan jaridar 12 a ranar Larabar makon da ya gabata zuwa yanzu an kai hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin Musulunci a sassa daban daban na kasar fiye da hamsin.
2700807