IQNA

Darul Ifta Na Masar Ya Yi Allawadai Da Zanen Batunci Na Jaridar Charlie Hebdo

12:57 - January 14, 2015
Lambar Labari: 2708555
Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta yi kakkausar suka dangane da yadda jaridar Charlie Hebdo tasake buga zanen batunci ga manzon Allah (SAW) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Libration cewa cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta yi kakkausar suka dangane da yadda jaridar Charlie Hebdo tasake buga zanen batunci ga manzon Allah (SAW) wanda hakan ya zama wani babban cin fuska ne.
Malamai da kungiyoyi daban-daban na musulmi na ci gaba da Allah wadai da sake buga wani zanen batanci ga Manzon Allah (s.a.w.a) da mujallar kasar Faransan nan mai suna Charlie Hebdo ta sake yi lamarin da a baya ma ya janyo fushin al’ummar musulmi har kuma ya sanya aka kai wa ofishinta hari a kwanakin baya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din na Talata, Cibiyar fatawa ta kasar Masar ta bayyana cewar buga irin wadannan zane wani neman tsokana da sosa ran sama da musulmi biliyan daya da rabi na duniya ne, tana mai jan kunnen cewa sake buga irin wannan zanen zai sake haifar da wani zaman dar-dar da kiyayya ne a tsakanin al’ummar kasar Faransa.
A jiya ne dai jaridar Charlie Hebdo din ta sanar da cewa za ta sake buga wani zanen batanci ga Ma’aikin Allah (s.a.w.a) a bugunta wanda zai fito a gobe Laraba lamarin da har ya zuwa yanzu babu wani abin da gwamnatin Faransan ta yi na hana faruwar hakan.
A ranar Larabar da ta gabata ce wasu mahara suka kai hari kan ofishin wannan jaridar da ke birnin Paris don nuna rashin amincewarsu da irin wannan cin mutumci da jaridar ta ke yi wa addinin Musulunci lamarin da yayi sanadiyyar kashe wasu mutane sha biyu.
2707463

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha