Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, a yau kungiyar Tauhid a Lebanon ta bayyana cewa abin da ya faru na kisan ‘yan gwagwarmaya na Hizbullah a Jolan ba zai tafi haka nan har sai an kwace palastinu da sauran yankunan da yahudawa suka mamaye.
A yammacin yau ne kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fara gudanar da jana’izar dakarun kungiyar su Shida da suka yi shahada a jiya Lahadi sakamakon harin da jiragen yakin HKI suka kai musu a yankin Quneitra da ke Tuddan Golan na kasar Siriya.
Tun a yammacin jiya ne kungiyar ta gudanar da jana’izar dan babban kwamandan sojin kungiyar Shahid Imad Mughniya, wanda shi ma yayi shahada a shekara ta dubu biyu da takwas.
A nasa bangaren shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hizbullah sayyid ne ya jagoranci sallar da aka yi wa shahid Jihad Imad Mughniyyan inda daga baya kuma dubun dubatan magoya bayan Hizbullah din suka raka gawar har zuwa makabartar shahidan kungiyar inda aka rufe shi kusa da kabarin mahaifin nasa a unguwar dhabiya da ke babban birnin kasar.
Kungiyar Hizbullah din ta sanar da shahadar dakaru shida daga cikin dakarunta sakamakon harin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai musu a lokacin da suke gudanar da rangadi a yankin Quneitra na kasar Siriya.
2735457