IQNA

Dubban Dalibai Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kare Martabar Ma’aiki A Sudan

16:59 - January 27, 2015
Lambar Labari: 2770306
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani babban gangami a birnin Khartum na kasar Sudan domin kare martabar ma’aiki da kuma la’antar jaridar da ke watsa zanen batunci ga manzo.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, a jiya dubban daliban makarantun sakandare da na jami’a sun gudanar da wani babban gangami a birnin Khartum na kasar Sudan domin kare martabar ma’aiki (SAW) da kuma la’antar jaridar Charlie Hebdo da ke watsa zanen batunci ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
An shirya gudanar da wannan gangami ne dai a gaban fadar shugaban kasar ta Sudan da ke birnin khartum, inda suka cika dukaknin titunan birnin suna rera taken cewa su baraden manzo ne na Khaibar, ma’ana masu shirin daukar fansa kan makiyansa.
Wannan jerin gwano ya jawo bababn cunkosoa  birnin khartum, inda aka yi ta nuna goyon bayan ga manzon Allah tare da sukar masu yada batunci gare shi da kuma addinin muslunci, da kuma rera taken cewa musulmi fansa ne gare shi.
2770047

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha