IQNA

Harin Yahudawa A kan Masallacin Birnin Quds Mai Alfarma

12:02 - February 05, 2015
Lambar Labari: 2812570
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya mazauna yankunan da suke mamaye da sun a palastinu sun kaddamar da farmaki kan masallacin aqsa mai alfarma.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Press TV cewa, ‘ya’yan kaka gida daga yahudawan sahyuniya mazauna yankunan da suke mamaye da sua  kusa da quds kai farmaki a masalalcin mai daraja.
Wani rahoton kuma yana cewa yanzu haka ana cikin halin zullumi a birnin Quds sakamakon tsauraran matakan da jami'an tsaron yahudawan Isra'ila suka dauka a birnin, bayan kiran da kungiyoyin gwagwarmaya suka yi kan gudanar da gangami da kuma bore a birnin da dukkanin biranan Palastinu.  
Rahotanni daga birnin sun tabbatar da cewa jami'an tsaron sun kafa shingaye a dukkanin tituna musamman masu isa masallacin Quds mai alfarma, duk kuwa da cewa a yau palastinawa sun samu damar gudanar da sallar juma'a a cikin masallacin, lamarin da yahudawan suka haramta musu a makonnin da suka gabata.
A bangaren guda kuma jami'an leken asirin na yahudawan Isra'ila sun kame wasu mambobin kungiyar Hamas a birnin na Quds, bisa zarginsu da tattara bayanai kan yadda ministocin harkokin wajen Isra'ila yake gudanar da harkokinsa, kama daga lokacin da yake fitowa daga gidansa, da kuma lokacin da yake isa ofishinsa, da kuma hanyoyin da yake bi.
2808328

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha