
KIamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Word Bulletin cewa, Malusi Gigaba na jam'iyyar ta ANC ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar a jiya, inda ta ce tana yin Allawadai da kakkausar murya kan wadannan hare-hare na wuce gona da iri a kan fararen hula marassa kariya, tare da kiran gwamnatin Isra'ila da ta dakatar da wannan danyen aiki ba tare da wani bata lokaci ba.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu ya sheda cewa, kisan fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da tsoffi da Isra'ila ke yi babban laifi ne bisa dukkanin dokoki na kasa da kasa.
Dubban mutane ne dai suka gudanar da zanga-zanga a biranan kasar daban daban domin yin Allawadai da hare-haren kisan kiyashi da Isra'ila da ke kaddamarwa kan al'ummar palastine.
Mai aiko ma tashar talabijin rahotanni daga biranan kasar ya ce mutanen da suka gudanar da jerin gwanon a yau sun haura mutane dubu dari inda suke rera take da ke yin kira ga gwamnatin kasar da ta yanke huldar diplomasiyyah da haramtacciyar kasar Isra'ila, kuma suna kwakwanta kisan kiyashin da ake yi wa palastinawa da cewa ya yi kama da irin wanda aka yi bakaken fata a lokacin mulkin wariyar launin fata da aka yi kasarsu.
Wasu daga cikin jagororin jam'iyyun siyasa da kungiyoyin lauyoyi da na malaman jami'a duk sun shiga jerin gwanon, wanda aka bayyana shi da cewa yana daya daga manyan jerin gwano da aka taba gudanarwa a tarihin kasar.
2819054