Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawabah News cewa, yanzu haka wasu daga cikin jagororin mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Masar suna kokarin kafa wata cibiya mai zaman kanta a kasar domin samun yancin gudanar da harkokinsu ba tare da wata tsangwama ba.
Wannan hankoro da shugabannin wasu daga cikin jam’iyyu da kuma kungiyoyi na mabiya mazhabar shi’a ke yi a Masar ya hada da karbar sa hannu mutane dubu 30 da suka amince da hakan, daga bisani kuma sai a kika dukkanin sunayen wadanda suka sanya hannu ga shugaban kasar AbdulFattah Sisi domin ya amince.
Idan har wannan shirin ya tabbata hakan zai baiwa mabiya mazhabar shi’a a Masar damar kafa wata babbar cibiyar wadda take da damar gudanar da harkokinta na siyasa da ilimi da zamantakewa a hukumance ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba kamar yadda take fuskanta a halin yanzu.
Babban abin da ya kara karfafa gwiwarsu domin yin hakan shi ne yadda mabiya akidar nan ta salafiya sukan yi shishigi a kansu ba tare da an dauki wani mataki na bin kadun hakkinsu ba a hukumance.