Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yabiladi cewa, tun kimanin watanni 3 da suka gabata ne mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Moroccoa garin Tanja suka fara gudanar da harkokinsu tare da izini.
Bayanin ya ci gaba da cewa bayan daukar dogon lokaci mabiya tafarkin iyalan gidan manzo suna fuskantar takura a garin, amma a halin yanzu sun samu takardun lasisi domin gudanar da ayyukansu da harkokinsu a cikin yanci.
Wanann dais hi ne karon farko da suke samun wananna damar wadda za ta sanya su gudanar da harkokinsu ba tare da wata takura a ba a garin, wanda kuma daya daga cikin manyan birane na ilimi da al'adun muslunci.
Mabiya tarafikin iyalan gidana manzo a Morocco suna cikin marassa rinjanye a a kasar da suke gudanar da harkokinsu a cikin takura.