IQNA

An Fara Shirin Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta 22 A Kasar Masar

16:55 - February 17, 2015
Lambar Labari: 2861945
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da shirin gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Masar a cikin watanni biyu masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews ya habarta cewa, yanzu haka an fara gudanar da shirin gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Masar wadda ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen ketare.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann gasa tana daya daga cikin manyan gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa  akasashen duniya, musamman ma ganin cewa Masar a daga cikin kasashe da kan gaba wajen karatu kur'ani a duniya.

Ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ita kan dauki nauyin shirya wannan gasa, inda kwamitin da ke kula da harkokin kur'ani a kasar da ake kallafa wa shirya gasar kan gayyaci makaranta da mahardata daga sassa na duniya.

Tuni kasashen da suke halartar gasar suka fara bayyana shirinsu na halartar gasar domin karawa da takwarorinsu na sauran kasashe, wanda kuma hakan na da babban tasiri matuka wajen kara zaburar da matasa wajen bayar da himma ga lamurran kur'ani.

Gasar za ta samu halrtar alkalai daga kasashen musulmi da kuma larabawa, wanda su ne za su tantance wadanda su matakai na daya da na biyu da kuma uku a adukkanin bangarorin gasar.

2858483

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha