IQNA

Gungun 14 Ga Fabrairu Ya yi Allawadai Da Cin Zarafin Malamin Shi'a A Bahrain

23:23 - February 20, 2015
Lambar Labari: 2874716
Bangaren kasa da kasa, gungun matasan 14 ga watan Fabrairu na kasar Bahrain sun fitar da bayanin yin Allah wadai da gidan sarautar Al Khalifah kan cin zarafin Sheikh Al-jid Alhafsi daya daga cikin manyan malaman shi'a a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 14 Fabrayer.com cewa, matasan 14 ga watan Fabrairu na kasar Bahrain sun fitar da bayanin yin Allah wadai da gidan sarautar kasar dangane da cin zarafin Sheikh Al-jid Alhafsi daya da ke yankin Al-sabus na kasar.

Dubban mutane sun gudanar da jerin a gwano a sassa daban-daban na kasar Bahrain, domin yin Allawadai da kakkausar murya dangane da cin zarafin wannan daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar Sheikh Al-jid Alhafsi da jami'an tsaron kasar suka yi.

Wadanda suka gdanar da jerin gwanon suna dauke da hotunan shehin malamin da kuma kyallaye da aka yi rubutu a kansu, da ke yin Allawadai da gidan sarautar kasar, da ke cin zarafin fararen hular kasar da ke neman a yi a dalci da gaskiya a cikin sha'anin mulki da siyasar kasar, maimakon mayar al'umma saniyar ware, ta yadda sarki da 'ya'yansa da mukarrabasa ne kawai suke da ikon mulki da kuma mallakar arzikin kasa.

Masu jerin gwanon sun sha alwashin cewa ba za su taba amincewa da cin zarafin malamai da ke fada wa sarakuna da masu mulki gaskiya ba, haka nan kuma masu zanga-zangar sun kirayi masarautar kasar da ta gaggauta sakin shugaban jam'iyyar Hadaka ta alwifagh Sheikh Ali Salman, wanda ake tsare da shi sakamakon gwagwarmayar nema wa talakawan kasar 'yancinsu, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa suna ci gaba da yin kiraye-kiraye ga masauar Bahrain da ta gaggauta sakin Sheikh Salman da ma sauran fursunonin siyasa da take tsare da su.
2872607

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha