Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar daga kasar Lebanon cewa, a jiya daruruwan malaman addinai sun gudanar da wani gangami da jerin gwano a birnin London domin yin kira zuwa ga sulhu dea zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya.
Wannan na daya daga cikin abin jagororin mabiya addina suka hadu a kansa domin jan hakulan mabiyansu da su zama cikin fadaka danagne da abubuwan da suke faruwa a halin yanzu, tun bayan bullar ayyukan ta’addanci da wasu ke yi da su addini.
Ko shakka babu wannan lamari yana da matukar tasiri ga mabiya addinai na muslunci da kiristanci musaman, bisda la’akari da cewa suna da fahimtar juna a kan batutuwa da dama, kuma malamai daga sassa na duniya na tattaunawa da mabiyasu a cikin wadannan addinai guda biyu, kamar yadda su ma yahudawa masu sassaucin ra’ayi ba a bar su a baya ba.
Za a ci gaba da bin wanann hanya a birtaniya da sauran kasashen turai domin kalubalantar masu kokarin haddasa fitina tsakanin mabiya addinai, kamar yadda dukkanin bangarorin kuma suka Allah wadai da ayyukan ta’addanci daga kowane bangare ya fito.
2872591